Hausa of Nigeria

Yahaya

Yahaya 1

Kalman ya Zama Mutum

1 Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. 2 Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah. 3 Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. 4 Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5 Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba. 6 Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya. 7 Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa. 8 Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken. 9 Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum. 10 Dā yana duniyar ma ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. 11 Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'arsa kuwa ba ta karɓe shi ba. 12 Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah, 13 wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah. 14 Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa. 15 Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ” 16 Dukanmu kuwa daga falalarsa muka samu, alheri kan alheri. 17 Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance. 18 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.

Shaidar Yahaya Maibaftisma

19 Wannan kuwa ita ce shaidar Yahaya, wato, sa'ad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, ko shi wane ne. 20 Sai ya faɗi gaskiya, bai yi m�su ba, gaskiya ya faɗa ya ce, “Ba ni ne Almasihu ba.” 21 Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A'a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A'a.” 22 Sai suka ce masa, “To, wane ne kai, domin mu sami amsar da za mu mayar wa waɗanda suka aiko mu? Me kake ce da kanka?” 23 Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku gyara wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.” 24 Su kuwa, Farisiyawa ne suka aiko su. 25 Sai suka tambaye shi suka ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?” 26 Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba, 27 shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in kwance ba.” 28 An yi wannan a Betanya ne, a hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma. 1 .29 “Ga Ɗan Rago na Allah” “Ga Ɗan Rago na Allah” 29 Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya! 30 Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ 31 Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra'ila na zo, nake baftisma da ruwa.” 32 Yahaya ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu na saukowa kamar kurciya daga sama, ya kasance a kansa. 33 Dā kam, ban san shi ba, shi dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ 34 Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa, wannan Ɗan Allah ne.”

Almajiran Yesu na Farko

35 Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu. 36 Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!” 37 Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suke bi Yesu. 38 Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato, Malam ke nan, ina kake da zama?” 39 Sai ya ce musu, “Ku zo ku gani.” Sai suka je suka ga inda yake da zama, suka kuwa yini tare da shi. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ne kuwa. 40 Ɗaya daga cikin biyun nan da suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan'uwan Bitrus. 41 Sai ya fara nemo ɗan'uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato, shafaffe. 42 Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato, kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato, Bitrus.

Yesu ya Kira Filibus da Nata'ala

43 Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.” 44 Filibus kuwa mutumin Betsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus. 45 Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato, Yesu Banazare, ɗan Yusufu.” 46 Nata'ala ya ce masa, “A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?” Sai Filibus ya ce masa, “Taho dai, ka gani.” 47 Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba'isra'ile na gaske wanda ba shi da ha'inci!” 48 Nata'ala ya ce masa, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'ad da kake gindin ɓaure, na gan ka.” 49 Sai Nata'ala ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!” 50 Yesu ya amsa ya ce, “Wato, domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure ne kake ba da gaskiya? Ai, za ka ga al'amuran da suka fi haka ma.” 51 Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”

Yahaya 2

Biki a Kana ta Galili

1 A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana nan, 2 aka kuma gayyaci Yesu da almajiransa. 3 Da ruwan inabi ya gaza, mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.” 4 Yesu ya ce mata, “Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.” 5 Sai mahaifiyar Yesu ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.” 6 A wurin kuwa akwai randuna shida na dutse a ajijjiye, bisa ga al'adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce tana cin wajen tulu shida shida. 7 Sai Yesu ya ce musu, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal. 8 Sa'an nan ya ce musu, “To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka kai. 9 Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), ya yi magana da ango, 10 ya ce, “Kowa, ai, kyakkyawan ruwan inabi yakan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa'an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!” 11 Wannan ce mu'ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi. 12 Bayan haka sai ya tafi Kafarnahum, da shi da mahaifiyarsa, da 'yan'uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can 'yan kwanaki.

Yesu ya Tsabtace Haikali

13 Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima. 14 A cikin Haikali ya sami waɗansu dillalan shanu, da na tumaki, da na tattabarai, da kuma 'yan canjin kuɗi zaune wurin aikinsu. 15 Sai ya tufka bulala mai harsuna ta igiya, ya kore su duka daga Haikalin, har da tumakin da shanun, ya kuma watsar da kuɗin 'yan canjin, ya birkice teburorinsu. 16 Ya ce da dillalan tattabarai, “Ku kwashe waɗannan daga nan, kada ku mai da Haikalin Ubana kasuwa.” 17 Sai almajiransa suka tuna a rubuce yake cewa, “Kishin Haikalinka ya ci raina matuƙa.” 18 Sai Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Wace mu'ujiza za ka nuna mana da kake haka?” 19 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe Haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.” 20 Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba'in da shida ana ginin Haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka ta da shi?” 21 Amma haikalin da Yesu ya ambata jikinsa ne. 22 Saboda haka bayan an tashe shi daga matattu, almajiransa suka tuna ya faɗi haka, suka kuma gaskata Nassi da maganar da Yesu ya faɗa.

Yesu ya San Zuciyar Kowa

23 To, sa'ad da yake Urushalima lokacin Idin Ƙetarewa, mutane da yawa suka gaskata da sunansa, saboda ganin mu'ujizan da ya yi. 24 Yesu bai amince da su ba, 25 domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da yake zuciyar ɗan adam.

Yahaya 3

Yesu da Nikodimu

1 To, akwai wani Bafarisiye, sunansa Nikodimu, wani shugaban Yahudawa. 2 Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu'ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.” 3 Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.” 4 Nikodimu ya ce masa, “Ƙaƙa za a haifi mutum bayan ya tsufa? Wato, ya iya komawa a cikin mahaifiyarsa ta sāke haifo shi?” 5 Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta wurin ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba. 6 Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne. 7 Kada ka yi mamaki domin na ce maka, ‘Dole a sāke haifarku.’ 8 Iska tana busawa inda ta ga dama. Kakan ji motsinta, amma ba ka san inda ta fito da inda za ta ba. Haka fa yake ga duk wanda Ruhu ya haifa.” 9 Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, “Ƙaƙa wannan zai yiwu?” 10 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra'ila, ba ka fahimci waɗannan al'amura ba? 11 Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu. 12 In na yi muku zancen al'amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al'amuran sama? 13 Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga Sama, wato, Ɗan Mutum (da yake Sama). 14 Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, 15 domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami. 16 “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai ba da gaskiya ba, an riga an yi masa hukunci, domin bai gaskata da sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19 Hukuncin kuwa shi ne, haske ya shigo duniya, amma mutane suka fi ƙaunar duhu da hasken, don ayyukansu mugaye ne. 20 Duk mai yin rashin gaskiya yakan ƙi hasken, ba ya kuma zuwa wajen hasken, don kada ayyukansa su tonu. 21 Mai aikata gaskiya kuwa yakan zo wajen hasken, domin a bayyana ayyukansa, cewa, da taimakon Allah ne aka yi su.”

Shi lalle ya Riƙa Ƙaruwa, ni kuwa Raguwa

22 Bayan haka, Yesu da almajiransa suka tafi ƙasar Yahudiya. A nan ya jima da su, yana yin baftisma. 23 Yahaya kuma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salima, domin da ruwa da yawa a can. Mutane kuwa suka yi ta zuwa ana yi musu baftisma. 24 Domin a sa'an nan ba a sa Yahaya a kurkuku ba tukuna. 25 Sai fa almajiran Yahaya suka tasar wa wani Bayahude da muhawwara a kan maganar tsarkakewa. 26 Suka kuma zo wurin Yahaya, suka ce masa, “Ya shugaba, wanda dā kuke tare a hayin Kogin Urdun, wanda kai kanka ma ka shaida shi, to, ga shi, yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa.” 27 Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga Sama. 28 Ku kanku ma shaiduna ne a kan na ce ba ni ne Almasihu ba, amma an aiko ni ne ni riga shi gaba. 29 Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron maganarsa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika. 30 Shi kam, lalle ne ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa.

Wanda ya Zo daga Sama

31 “Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa. 32 Abin da ya ji, ya kuma gani, shi yake shaidarwa, duk da haka ba wanda yake yarda da shaidarsa. 33 Duk wanda ya yarda da shaidarsa, ya haƙƙaƙe, cewa, Allah mai gaskiya ne. 34 Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba. 35 Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa. 36 Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi.”

Yahaya 4

Yesu da wata Basamariya

1 To, da Ubangiji Yesu ya sani dai Farisiyawa sun ji labari yana samun almajirai, yana kuma yi musu baftisma fiye da Yahaya 2 (ko da yake dai ba Yesu kansa yake yin baftisma ba, almajiransa ne), 3 sai ya bar ƙasar Yahudiya, ya koma ƙasar Galili. 4 Lalle ne kuwa yă ratsa ƙasar Samariya. 5 Sai ya zo wani gari na ƙasar Samariya, wanda ake kira Saikar, kusa da yankin ƙasar da Yakubu ya ba ɗansa Yusufu. 6 Rijiyar Yakubu kuwa a nan take. Saboda gajiyar tafiya fa, sai Yesu ya zauna haka nan a bakin rijiyar. Wajen tsakar rana ce kuwa. 7 Sai ga wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa. Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha.” 8 Almajiransa kuwa sun shiga gari sayen abinci. 9 Sai Basamariyar ta ce masa, “Ƙaƙa kai Bayahude za ka roƙe ni ruwan sha, ni da nake Basamariya?” (Don Yahudawa ba sa cuɗanya da Samariyawa). 10 Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Ba ni ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.” 11 Sai matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ai, ba ka da guga, rijiyar kuwa da zurfi. To, ina ka sami ruwan nan na rai? 12 Ashe, ka fi ubanmu Yakubu ne, wanda ya bar mana rijiyar, har shi da kansa, da 'yayansa, da dabbobinsa, suka sha ruwanta?” 13 Yesu ya amsa mata ya ce, “Duk mai shan ruwan nan zai sāke jin ƙishirwa. 14 Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.” 15 Macen ta ce masa, “Ya Shugaba, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, kada kuma in riƙa zuwa har nan in ɗiba.” 16 Sai Yesu ya ce mata, “Je ki, ku zo da mijinki.” 17 Sai macen ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji, 18 don kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.” 19 Macen ta ce masa, “Ya Shugaba, na dai gane kai annabi ne. 20 Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan. Ku kuwa kun ce a Urushalima ne wurin da ya wajaba a yi sujada.” 21 Sai Yesu ya ce da ita, “Mace, ki gaskata ni, lokaci na zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ba, ko a kan dutsen nan, ko a Urushalima, 22 Ku kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada, mu kuwa muna yi wa abin da muka sani sujada, domin ceto ta hanyar Yahudawa yake. 23 Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a ruhu, da gaskiya kuma. Lalle kuwa irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. 24 Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.” 25 Sai macen ta ce masa, “Na san Almasihu yana zuwa, (wanda ake kira Kristi). Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.” 26 Yesu ya ce mata, “Ni ne, ni mai maganar nan da ke.” 27 Ya gama magana ke nan sai almajiransa suka iso. Suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma kuwa ba wanda ya ce, “Me kike bukata?” ko, “Don me kake magana da ita?” 28 Sai matar ta bar tulunta, ta koma gari, ta ce wa mutane, 29 “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin, ko wannan shi ne Almasihu?” 30 Sai suka fito daga garin suka nufo shi. 31 Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Malam, ci abinci.” 32 Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.” 33 Almajiran suka ce wa juna, “Shin, wani ya kawo masa abinci ne?” 34 Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa. 35 Ba kuna cewa, kaka saura wata huɗu ba? Ina gaya muku fa, ku duba gonaki, ku gani, sun nuna sun isa girbi. 36 Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. 37 A nan kam, wannan karin maganar gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani da girbi.’ 38 Na aike ku girbin abin da ba ku yi wahalarsa ba. Waɗansu sun yi wahala, ku kuwa kun mori wahalarsu.” 39 Samariyawa da yawa na wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” 40 Da samariyawa suka iso wurinsa, suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. Ya kuwa kwana biyu a nan. 41 Saboda maganarsa kuma waɗansu da yawa suka gaskata. 42 Sa'an nan suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, domin mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Mai Ceton duniya.”

Yesu ya Warkar da Ɗan Basarake

43 Bayan kwana biyun nan sai ya tashi daga nan ya tafi ƙasar Galili. 44 Domin Yesu kansa ya yi shaida cewa, annabi ba shi da girma a garinsu. 45 Da ya isa ƙasar Galili, sai Galilawa suka yi na'am da shi, domin sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin idi, domin su ma sun je idin. 46 Sai ya sāke zuwa Kana ta ƙasar Galili, inda ya mai da ruwa ruwan inabi. A Kafarnahum kuwa akwai wani basarake wanda ɗansa ba shi da lafiya. 47 Da jin cewa, Yesu ya fito ƙasar Yahudiya ya komo ƙasar Galili, sai ya tafi wurinsa, ya roƙe shi ya je ya warkar da ɗansa, don yana bakin mutuwa. 48 Yesu ya ce masa, “In ba mu'ujizai da abubuwan al'ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.” 49 Sai basaraken nan ya ce masa, “Ya Shugaba, ka zo tun ƙaramin ɗana bai mutu ba.” 50 Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, ɗanka a raye yake.” Mutumin kuwa ya gaskata maganar da Yesu ya faɗa masa, ya yi tafiyarsa. 51 Yana cikin tafiya sai ga barorinsa sun taryo shi, suka ce masa, “Ɗanka ya warke.” 52 Sai ya tambaye su ainihin lokacin da ya fara samun sauƙi. Suka ce masa, “Jiya da ƙarfe ɗaya da rana zazzaɓin ya sake shi.” 53 Sai uban ya gane, daidai lokacin nan ne, Yesu ya ce masa, “Ɗanka a raye yake.” Shi da kansa kuwa ya ba da gaskiya, da jama'ar gidansa duka. 54 Wannan kuwa ita ce mu'ujiza ta biyu da Yesu ya yi a Galili, bayan komowarsa daga Yahudiya.

Yahaya 5

Warkarwa a Tafkin Betasda

1 Bayan haka sai Yesu ya tafi Urushalima domin idin Yahudawa. 2 A Urushalima, kusa da Ƙofar Tumaki, akwai wani ruwa da ake ce da shi Betasda da Yahudanci, an kuwa kewaye shi da shirayi biyar. 3 A shirayin nan kuwa marasa lafiya da yawa sun saba kwanciya, makafi, da guragu, da shanyayyu.Suna jira a motsa ruwan. 4 Don lokaci lokaci wani mala'ika yakan sauko cikin ruwan ya motsa shi. Duk kuwa wanda ya fara shiga bayan an motsa ruwan, sai ya warke daga duk irin cutar da yake da ita. 5 A nan kuwa akwai wani mutum da ya shekara talatin da takwas da rashin lafiya. 6 Da Yesu ya gan shi kwance, ya kuma sani ya daɗe da wannan hali, sai ya ce masa, “Kana so a warkar da kai?” 7 Marar lafiyar ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, ai, ba ni da wanda zai saka ni cikin ruwan lokacin da aka motsa shi. Lokacin da na doshi ruwan kuma sai wani ya riga ni shiga.” 8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi!” 9 Nan take mutumin ya warke, ya ɗauki shimfiɗarsa ya yi tafiyarsa. Ran nan kuwa Asabar ce. 10 Saboda haka Yahudawa suka ce da wanda aka warkar ɗin, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka ɗauki shimfiɗarka ba.” 11 Sai ya amsa musu ya ce, “Ai, wanda ya warkar da ni, shi ne ya ce in ɗauki shimfiɗata, in tafi.” 12 Suka tambaye shi, “Wanne mutum ne ya ce maka ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi?” 13 Wanda aka warkar ɗin kuwa bai san ko wane ne ba, domin Yesu ya riga ya tashi saboda taron da suke wurin. 14 Bayan haka Yesu ya same shi a Haikali, ya ce masa, “Ka ga fa, ka warke! To, ka daina yin zunubi, don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.” 15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahudawa, Yesu ne ya warkar da shi. 16 Saboda haka, Yahudawa suka fara tsananta wa Yesu, don yana yin irin waɗannan abubuwa ran Asabar. 17 Yesu kuwa ya amsa musu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina yi.” 18 Don haka, Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi, ba don ya keta Asabar kaɗai ba, har ma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato, yana daidaita kansa da Allah.

Ikon Ɗan

19 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, Ɗan ba ya yin kome shi kaɗai, sai abin da ya ga Uba yana yi. Domin duk abin da Uban yake yi, haka shi Ɗan ma yake yi. 20 Domin Uban na ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa yake yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, domin ku yi al'ajabi. 21 Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa. 22 Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan, 23 domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan. 24 Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai. 25 “Lalle hakika, ina gaya muku, lokaci yana zuwa, har ma ya yi, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, masu ji kuwa su rayu. 26 Yadda Uba kansa yake tushen rai, haka ya sa Ɗan ya zama tushen rai. 27 Ya kuma ba shi ikon zartar da hukunci, saboda shi Ɗan Mutum ne. 28 Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke kaburbura za su ji muryarsa, 29 su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta su tashi, tashin rai, waɗanda suka yi rashin gaskiya kuwa su tashi, tashin hukunci.

Shaidun Yesu

30 “Ba na iya yin kome ni kaɗai. Yadda nake ji, haka nake yin hukunci. Hukuncina kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 31 In na shaida kaina, shaidata ba tabbatacciya ba ce. 32 Akwai wani mashaidina dabam, na kuwa san shaidar da yake yi a kaina tabbatacciya ce. 33 Kun aika wajen Yahaya, shi kuma ya shaidi gaskiya. 34 Duk da haka shaidar da na dogara da ita ba ta mutum ba ce. Na dai faɗi haka ne domin ku sami ceto. 35 Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan. 36 Amma shaidar da ni nake da ita ta fi ta Yahaya ƙarfi. Domin ayyukan da Uba ya ba ni in gama, su ainihin ayyukan nan da nake yi, ai, su ne shaidata a kan cewa, Uba ne ya aiko ni. 37 Uban kuma da ya aiko ni, shi kansa ya shaide ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ba, ko ganin kama tasa. 38 Maganarsa kuwa ba ta zauna a zuciyarku ba, domin ba ku gaskata wanda ya aiko ba. 39 Kuna ta nazarin Littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata. 40 Duk da haka, kun ƙi zuwa wurina ku sami rai. 41 Ba na karɓar girma wurin mutane. 42 Amma fa na san ku, ba ku da ƙaunar Allah a zuci. 43 Ni na zo ne da sunan Ubana, ga shi, ba ku karɓe ni ba. In da wani zai zo da sunan kansa, shi za ku karɓa. 44 Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karɓar girma a junanku, girman da yake daga Allah Makaɗaici kuwa, ba kwa nemansa? 45 Kada ku zaci zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi. 46 Da dai kun gaskata Musa, da kun gaskata ni, domin labarina ya rubuta. 47 In kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”

Yahaya 6

Ciyar da Mutum Dubu Biyar

1 Bayan haka Yesu ya haye Tekun Galili, wato, Tekun Tibariya. 2 Sai taro mai yawa suka bi shi, don sun ga mu'ujizan da yake yi ga marasa lafiya. 3 Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa. 4 To, Idin Ƙetarewa wato, idin Yahudawa, ya gabato. 5 Da Yesu ya ɗaga kai ya hango babban taro yana doso shi, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayo gurasar da mutanen nan za su ci?” 6 Ya faɗi haka ne fa domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi. 7 Filibus ya amsa ya ce, “Ai, ko gurasar dinari metan ma ba ta isa ko wannensu ya sami kaɗan ba.” 8 Sai Andarawas ɗan'uwan Bitrus ɗaya daga cikin almajiransa, ya ce masa, 9 “Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha'ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?” 10 Yesu ya ce, “Ku ce wa mutane su zauna.” Wuri ne kuwa mai ciyawa. Sai mazaje suka zazzauna, su wajen dubu biyar. 11 Yesu ya ɗauki gurasar, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa waɗanda suke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su. 12 Da suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka saura, kada kome ya lalace.” 13 Sai suka tattara gutsattsarin gurasar nan biyar na sha'ir da suka saura bayan kowa ya ci, suka cika kwando goma sha biyu. 14 Da jama'a suka ga mu'ujizar da ya yi, suka ce, “Lalle, wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya!” 15 Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yayi su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa a kan dutsen shi kaɗai.

Yesu na Tafiya a kan Ruwan Teku

16 Da magariba ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa teku. 17 Suka shiga jirgi suka tasar wa haye tekun zuwa Kafarnahun. A sa'an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna. 18 Sai tekun ta fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da take busowa. 19 Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita. 20 Amma ya ce musu, “Ni ne, kada ku ji tsoro.” 21 Sa'an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin. Nan da nan sai ga jirgin a gāɓar da za su.

Taro sun Nemi Yesu

22 Kashegari sauran taron da suka tsaya a hayin tekun suka lura ba wani jirgi a wurin, sai ɗan ƙarami, suka kuma lura Yesu bai shiga cikinsa tare da almajiransa ba, sai almajiran ne kaɗai suka tafi. 23 Akwai kuwa waɗansu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da taron suka ci gurasa bayan Ubangiji ya yi godiya. 24 Sa'ad da kuwa taron suka ga ba Yesu, ba almajiransa a nan, su ma suka shiga ƙananan jiragen, suka tafi Kafarnahum neman Yesu.

Yesu Gurasar Rai

25 Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Ya Shugaba, yaushe ka zo nan?” 26 Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu'ujizai ba, sai don kun ci gurasar nan kun ƙoshi. 27 Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato, Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.” 28 Sai suka ce masa, “Me za mu yi mu aikata ayyukan da Allah yake so?” 29 Yesu ya amsa musu ya ce, “Wannan shi ne aikin da Allah yake so, wato, ku gaskata da wanda ya aiko.” 30 Sai suka ce masa, “To, wace mu'ujiza za ka yi mu gani mu gaskata ka? Me za ka yi? 31 Kakannin kakanninmu sun ci manna a jeji, yadda yake a rubuce cewa, ‘Ya ba su gurasa daga Sama su ci.’ ” 32 Sa'an nan Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ba Musa ne ya ba ku gurasar nan daga Sama ba, Ubana ne yake ba ku hakikanin Gurasa daga Sama. 33 Ai, Gurasar Allah shi ne mai saukowa daga Sama, mai ba duniya rai.” 34 Sai suka ce masa, “Ya Ubangiji, ka riƙa ba mu irin wannan gurasa kullum!” 35 Yesu ya ce musu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. 36 Na dai gaya muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba. 37 Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan. 38 Domin na sauko daga Sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 39 Nufin wanda ya aiko ni kuwa, shi ne kada in yar da kowa daga cikin dukkan waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a ranar ƙarshe. 40 Gama nufin Ubana, shi ne duk wanda yake duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da shi, yă sami rai madawwani, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe.” 41 Sai fa Yahudawa suka yi masa gunaguni, domin ya ce, “Ni ne Gurasar da ya sauko daga Sama.” 42 Suka ce, “Ashe, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusufu, wanda mahaifiyarsa da mahaifinsa duk mun san su? To, yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko ne daga sama?’ ” 43 Yesu ya amsa musu ya ce, “Kada ku yi gunaguni a junanku. 44 Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe. 45 A rubuce yake cikin littafan annabawa cewa, ‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni. 46 Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda yake daga wurin Allah, shi ne ya ga Uban. 47 Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami. 48 Ni ne Gurasa mai ba da rai. 49 Kakannin kakanninku sun ci manna a jeji, amma kuwa sun mutu. 50 Ga Gurasa mai saukowa daga Sama, domin kowa yă ci, kada ya mutu. 51 Ni ne Gurasar rai da ya sauko daga Sama. Kowa ya ci Gurasan nan, zai rayu har abada. Har ma gurasar da zan bayar naman jikina ne, domin duniya ta rayu.” 52 Sai Yahudawa suka ta da husuma a junansu, suna cewa, “Yaya mutumin nan zai iya ba mu naman jikinsa mu ci?” 53 Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku. 54 Duk wanda yake cin naman jikina, yake kuma shan jinina, yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe. 55 Domin naman jikina abinci ne na hakika, jinina kuma abin sha ne na hakika. 56 Duk wanda yake cin naman jikina, yake shan jinina, a cikina yake zaune, ni kuma a cikinsa. 57 Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni. 58 Wannan shi ne Gurasar da ya sauko daga Sama, ba irin wadda kakannin kakanninku suka ci ba, duk da haka suka mutu. Duk mai cin Gurasan nan zai rayu har abada.” 59 Wannan kuwa a majami'a ya faɗa, sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum.

Kalmomin Rai

60 Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan magana mai wuya ce, wa zai iya jinta?” 61 Yesu kuwa, da yake ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato, wannan ne ya zamar muku abin tuntuɓe? 62 Yaya ke nan in kuka ga Ɗan Mutum yana hawa inda yake dā? 63 Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai. 64 Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi. 65 Sai ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku, ba mai iya zuwa gare ni, sai ko Uba ya yardar masa.” 66 Kan wannan da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba. 67 Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, “Ku ma kuna so ku tafi ne?” 68 Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? Kai kake da maganar rai madawwami. 69 Mu kuwa mun gaskata, mun kuma tabbata kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.” 70 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ni na zaɓe ku, ku goma sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.” 71 Wato, yana nufin Yahuza, ɗan Saminu Iskariyoti, don shi ne zai bāshe shi, ko da yake ɗaya daga cikin goma sha biyun nan ne.

Yahaya 7

'Yan'uwan Yesu ba su Gaskata da shi Ba

1 Bayan haka, Yesu ya riƙa zagawa a Ƙasar Galili, bai yarda ya zaga ta Yahudiya ba, don Yahudawa suna neman kashe shi. 2 Idin Bukkoki na Yahudawa kuwa ya gabato. 3 Sai 'yan'uwansa suka ce masa, “Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya, almajiranka su ma su ga ayyukan da kake yi. 4 Ai, ba mai aiki a ɓoye in yana so ya shahara. Tun da yake kana yin waɗannan al'amura, to, sai ka bayyana kanka ga duniya.” 5 Domin ko dā ma 'yan'uwansa ba su gaskata da shi ba. 6 Sai Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna, amma ku, koyaushe lokacinku ne. 7 Ba dama duniya ta ƙi ku, amma ni take ƙi, don na shaide ta a kan ayyukanta mugaye ne. 8 Ku dai ku tafi idin. Ni ba za ni ba yanzu, don lokacina bai yi sosai ba tukuna.” 9 Da ya faɗa musu haka, ya dakata a ƙasar Galili.

Yesu a Idin Bukkoki

10 Bayan 'yan'uwansa sun tafi idin kuwa, shi ma ya tafi, amma a ɓoye, ba a fili ba. 11 Yahudawa suna ta nemansa a wurin idin suna cewa, “Ina yake ne?” 12 Taro kuma suka riƙa maganarsa a raɗe, waɗansu suna cewa, “Mutum ne nagari.” Waɗansu kuma suna cewa, “A'a, ai, ɓad da jama'a yake.” 13 Amma ba wanda ya yi maganarsa a fili don tsoron Yahudawa. 14 Wajen tsakiyar idin sai Yesu ya shiga Haikali ya koyar. 15 Yahudawa suka yi mamakin abin, suka ce, “Yaya mutumin nan yake da karatu haka, ga shi kuwa, bai taɓa koyo ba?” 16 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta wanda ya aiko ni ce. 17 Duk mai son aikata nufin Allah zai san koyarwar nan ko ta Allah ce, ko domin kaina nake faɗa. 18 Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi. 19 Ashe, ba Musa ne ya ba ku Shari'a ba? Duk da haka ba mai kiyaye Shari'ar a cikinku. Don me kuke neman kashe ni?” 20 Taron suka amsa suka ce, “Kana da iska! Wa yake neman kashe ka?” 21 Yesu ya amsa musu ya ce, “Aiki ɗaya kawai na yi, dukanku kuwa kuna mamakinsa. 22 Musa ya bar muku kaciya, (ba ko shi ya fara ba, tun kakannin kakanni ne), ga shi kuma, kukan yi wa mutum kaciya ko a ran Asabar ma. 23 To, in ana yi wa mutum kaciya ran Asabar don gudun keta Shari'ar Musa, kwa yi fushi don na warkar da mutum sarai ran Asabar? 24 Kada ku yi hukunci da zato, amma ku yi hukunci da adalci.” 7 .25 Wannan Almasihu Ne? Wannan Almasihu Ne? 25 Sai waɗansu mutanen Urushalima suka ce, “Ashe, ba wannan ne mutumin da suke nema su kashe ba? 26 Ga shi nan kuwa, yana magana a fili, ba su ce masa kome ba! Ya yiwu kuma shugabanni sun san lalle wannan shi ne Almasihu? 27 Wannan kam, mun san daga inda yake, amma sa'ad da Almasihu ya zo ba wanda zai san daga inda yake.” 28 Yesu yana koyarwa a Haikalin ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “Kun dai san ni, kun kuma san daga inda nake. Ban fa zo domin kaina ba. Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, shi kuwa ba ku san shi ba. 29 Ni na san shi, domin daga wurinsa na fito, shi ne kuwa ya aiko ni.” 30 Don haka suka nema su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna. 31 Duk da haka mutane da yawa cikin taron sun gaskata da shi, suna cewa, “Sa'ad da Almasihu ya zo, zai yi mu'ujizai fiye da na mutumin nan?”

An Aiki Dogaran Haikalin su Kamo Yesu

32 Farisiyawa suka ji taro suna raɗeraɗinsa haka, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki dogaran Haikali su kamo shi. 33 Sai Yesu ya ce, “Saurana ɗan lokaci kaɗan tare da ku, sa'an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni. 34 Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba. Inda nake kuwa ba za ku iya zuwa ba.” 35 Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina za shi da har ba za mu same shi ba? Za shi wurin Yahudawan da suka warwatsu a cikin al'ummai ne, ya koya wa al'umman? 36 Me kuma yake nufi da cewa, ‘Za ku neme ni amma ba za ku same ni ba?’ da kuma cewa, ‘Inda nake ba za ku iya zuwa ba?’ ”

Kogunan Ruwan Rai

37 A ranar ƙarshe ta idin, wato, babbar ranar, sai Yesu ya tsaya, ya ɗaga murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa yă zo gare ni yă sha. 38 Duk mai gaskatawa da ni, kamar yadda nassi ya ce, ‘Daga zuciyarsa ne kogunan ruwan rai za su gudana.’ ” 39 To, wannan shi ne ya faɗa game da Ruhu, wanda masu gaskatawa da shi za su karɓa, domin har yanzu ba a ba da Ruhu ba, saboda ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna.

Rabuwa ta Shiga Tsakanin Mutane

40 Da jin maganar nan waɗansu daga cikin taron suka ce, “Hakika wannan annabin nan ne.” 41 Waɗansu kuwa suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma waɗansu suka ce, “Me? Ashe, Almasihu daga ƙasar Galili zai fito? 42 Nassi ba cewa, ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?” 43 Sai kuma rabuwa ta shiga tsakaninsu a kansa. 44 Waɗansunsu suka so su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi.

Shugabanni ba su Gaskata da Yesu Ba

45 Daga nan dogaran Haikali suka koma wurin manyan firistoci da Farisiyawa, su kuwa suka ce musu, “Don me ba ku kawo shi ba?” 46 Sai dogaran suka amsa suka ce, “A'a, ba mutumin da ya taɓa magana kamar wannan!” 47 Sai Farisiyawa suka amsa musu suka ce, “Af! Har ku ma an ɓad da ku ne? 48 Ashe, akwai wani daga cikin shugabanni ko Farisiyawa da ya gaskata da shi? 49 Amma wannan taro da ba su san Attaura ba, ai, la'anannu ne.” 50 Nikodimu kuwa da ya je wurinsa dā, yana kuwa ɗaya daga cikinsu, ya ce musu, 51 “Ashe, shari'armu takan hukunta mutum tun ba a ji daga bakinsa ba, an kuma san abin da yake ciki?” 52 Suka amsa masa suka ce, “Kai ma Bagalile ne? Bincika mana ka gani, ai, ba wani annabi da zai bayyana a ƙasar Galili.”

Matar da aka Kama da Zina

53 Sai kowa ya tafi gida.

Yahaya 8

1 Yesu kuwa ya hau Dutsen Zaitun. 2 Da sassafe kuma ya sāke shiga Haikali. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu. 3 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka kawo wata mace da aka kama da zina. Da suka tsai da ita a tsaka, 4 suka ce masa, “Malam, matar nan an kama ta ne, suna cikin yin zina. 5 To, a Attaura Musa ya umarce mu mu kashe irin waɗannan da jifa, kai kuwa me ka ce?” 6 Sun faɗi haka ne don su gwada shi, ko sa sami hanyar kai ƙararsa. Amma Yesu ya sunkuya, ya yi ta rubutu a ƙasa da yatsa. 7 Da suka dinga tambayarsa sai ya ɗaga, ya ce musu, “To, marar zunubi a cikinku ya fara jifanta da dutse.” 8 Sai ya sāke sunkuyawa, ya yi ta rubutu a ƙasa. 9 Su kuwa da suka ji haka suka fita da ɗaya ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da matar a tsaye a wurin. 10 Sai Yesu ya ɗaga, ya ce mata, “Uwargida, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?” 11 Ta ce, “Babu, ya Ubangiji.” Sai Yesu ya ce, “Ni ma ban hukunta ki ba. Yi tafiyarki. Daga yau kada ki ƙara yin zunubi.”

Yesu Hasken Duniya

12 Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,” 13 Saboda haka Farisiyawa suka ce masa, “Kanka kake wa shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.” 14 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, domin na san inda na fito, da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ba, ko kuma inda za ni. 15 Ku kuna hukunci irin na duniya ne, ni kuwa ba na hukunta kowa. 16 Amma ko da zan yi hukunci, hukuncina na gaskiya ne, domin ba ni kaɗai nake ba, ni da Uba wanda ya aiko ni ne. 17 A Attaurarku ma a rubuce yake, cewa, shaidar mutum biyu tabbatacciya ce. 18 Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.” 19 Saboda haka suka ce masa, “Ina Uban naka yake?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko ni ko Ubana, ba wanda kuka sani. Da kun san ni, da kun san Ubana ma.” 20 Ya faɗi wannan magana ne a baitulmalin Haikali, lokacin da yake koyarwa a wurin. Duk da haka ba wanda ya kama shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.

Inda za ni ba ku iya Zuwa Ba

21 Sai ya ƙara ce musu, “Zan yi tafiya, za ku kuwa neme ni, amma za ku mutu da zunubinku. Inda za ni kuwa ba za ku iya zuwa ba.” 22 Saboda haka sai Yahudawa suka ce, “Wato, zai kashe kansa ke nan da ya ce, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba?’ ” 23 Sai ya ce musu, “Ku daga ƙasa kuke, ni kuwa daga sama nake. Ku na duniyar nan ne, ni kuwa ba na duniyar nan ba ne. 24 Shi ya sa na ce muku za ku mutu da zunubanku. Domin in ba ku gaskata ni ne shi ba, za ku mutu da zunubanku.” 25 Sai suka ce masa, “Kai wane ne?” Yesu ya ce musu, “Daidai yadda na gaya muku. 26 Akwai abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma shi wannan da ya aiko ni mai gaskiya ne. Abin da na jiyo daga gare shi kuwa, shi nake shaida wa duniya.” 27 Ba su gane maganar Uba yake yi musu ba. 28 Sai Yesu ya ce, “Sa'ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa'an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa. 29 Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni, bai bar ni ni kaɗai ba, domin koyaushe ina aikata abin da yake so.” 30 Sa'ad da Yesu yake faɗar haka, mutane da yawa suka gaskata da shi.

Gaskiya za ta 'Yanta Ku

31 Sai Yesu ya ce wa Yahudawan nan da suka gaskata shi, “In dai kun zauna kan maganata, hakika ku almajiraina ne. 32 Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta 'yanta ku.” 33 Suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya kuma za ka ce za a 'yanta mu?” 34 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai aikata zunubi bawan zunubi ne. 35 Ai, bawa ba ya ɗorewa a gida har abada, ɗa kuwa yana ɗorewa. 36 In kuwa Ɗan ya 'yanta ku, za ku 'yantu, 'yantuwar gaske. 37 Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku. 38 Ina faɗar abin da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abin da kuka ji daga wurin naku uban.”

Ubanku Iblis Ne

39 Suka amsa masa suka ce, “Ai, Ibrahim ne ubanmu.” Yesu ya ce musu, “Da ku 'ya'yan Ibrahim ne, da sai ku yi aikin da Ibrahim ya yi. 40 Ga shi yanzu, kuna neman kashe ni, ni mutumin da na gaya muku gaskiyar da na ji wurin Allah. Ba haka Ibrahim ya yi ba. 41 Ku kuna aikin da ubanku yake yi ne.” Suka ce masa, “Ba a haife mu daga fasikanci ba, ubanmu ɗaya ne, wato, Allah.” 42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, domin daga wurin Allah na fito, ga ni nan kuwa. Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni. 43 Don me ba kwa gane maganata? Don ba kwa iya jimirin jin maganata ne. 44 Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45 Amma domin ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni. 46 A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya nake faɗa, to, don me ba kwa gaskata ni? 47 Na Allah yakan saurari Maganar Allah. Abin da ya sa ba kwa sauraronta ke nan, don ku ba na Allah ba ne.”

Kafin Ibrahim, Nake

48 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe, gaskiyarmu da muka ce kai Basamariye ne, kana kuma da iska.” 49 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai iska ba ne. Ubana nake girmamawa, ku kuwa wulakanta ni kuke yi. 50 Ba ni nake nemar wa kaina girma ba, akwai mai nemar mini, shi ne kuma mai yin shari'a. 51 Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.” 52 Sai Yahudawa suka ce masa, “To, yanzu kam, mun tabbata kana da iska. Ai, Ibrahim ya mutu, haka ma annabawa, kana kuwa cewa, kowa ya kiyaye maganarka ba zai mutu ba har abada. 53 Wato, ka fi ubanmu Ibrahim ne, ya kuwa mutu? Annabawa ma sun mutu! Wa ka mai da kanka ne?” 54 Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba a bakin kome take ba. Ubana shi ne mai ɗaukaka ni, wanda kuke cewa, shi ne Allahnku. 55 Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da na ce ban san shi ba, da na zama maƙaryaci kamarku. Amma na san shi, ina kuma kiyaye maganarsa. 56 Ubanku Ibrahim ya yi farin ciki matuƙa ya sami ganin zamanina, ya kuwa gan shi, ya yi murna.” 57 Sai Yahudawa suka ce masa, “Har yanzu ma ba ka kai shekara hamsin ba, ashe ka ga Ibrahim!” 58 Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne.” 59 Don haka suka ɗebo duwatsu su jajjefe shi. Yesu kuwa ya ɓuya, ya fita daga Haikalin.

Yahaya 9

Warkar da wanda aka Haifa Makaho

1 Yesu yana wucewa sai ya ga wani mutum da aka haifa makaho. 2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, wa ya yi zunubi da aka haifi mutumin nan makaho, shi, ko iyayensa?” 3 Yesu ya amsa ya ce, “Ba domin mutumin nan ko iyayensa sun yi zunubi ba, sai domin a nuna aikin Allah ne a kansa. 4 Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa'ad da ba mai iya aiki. 5 Muddin ina duniya ni ne hasken duniya.” 6 Da ya faɗi haka sai ya tofa yau a ƙasa, ya cuɗa ƙasa, ya shafa a idanun makahon, 7 ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” (wato, aikakke). Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani. 8 Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?” 9 Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, kai dai, sun yi kama.” Shi kuwa ya ce, “Sosai ni ne!” 10 Sai suka ce masa, “To, ƙaƙa aka yi idanunka suka buɗe?” 11 Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke ido.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.” 12 Suka ce masa, “Ina yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”

Farisiyawa sun Bincika Labarin wanda aka Warkar

13 Sai suka kai wa Farisiyawa mutumin da yake makaho a dā. 14 To, ran Asabar ne Yesu ya cuɗa ƙasar ya buɗe masa ido. 15 Farisiyawa ma suka tambaye shi ta yadda aka yi ya sami gani. Ya ce musu, “Cuɗaɗɗiyar ƙasa ya shafa a idona, na wanke, ina gani.” 16 Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu'ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu. 17 Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.” 18 Yahudawa kam, ba su gaskata shi makaho ne a dā ba, ya kuma sami gani, har suka kira iyayen wanda ya sami ganin, 19 suka tambaye su suka ce, “Wannan ɗanku ne da kuke cewa, an haife shi makaho? To, ta yaya yake iya gani yanzu?” 20 Sai iyayen nasa suka amsa suka ce, “Mun dai san wannan ɗanmu ne, makaho ne aka haife shi. 21 Amma ta yadda aka yi yake gani yanzu ba mu sani ba, ba mu ma san wanda ya buɗe idon ba. Ku tambaye shi, ai, ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.” 22 Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa, kowa ya amsa, cewa, shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama'a. 23 Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, ba yaro ba ne, ku tambaye shi.” 24 Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.” 25 Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam, na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.” 26 Sai suka ce masa, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe maka ido?” 27 Ya amsa musu ya ce, “Na riga na faɗa muku, ba ku ji ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?” 28 Sai suka fāɗa shi da zagi, suna cewa, “Kai ne dai almajirin wannan ɗin, mu kam, almajiran Musa ne. 29 Mun dai sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan ba mu san ta inda ya fito ba.” 30 Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Yau ga abin mamaki! Ashe, ba ku san ta inda ya fito ba, ga shi kuwa, ya buɗe mini ido! 31 Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi. 32 Tun da aka fara duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba. 33 Da mutumin nan ba daga Allah ya fito ba, da ba abin da zai iya yi.” 34 Suka amsa masa suka ce, “Kai da aka haifa a baƙin zunubi ne za ka koya mana?” Sai suka kore shi.

Makanta ta Ruhu

35 Yesu ya ji labari sun kore shi. Da ya same shi, ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum ko?” 36 Ya amsa ya ce, “Wane ne shi, ya Shugaba, da zan gaskata da shi?” 37 Yesu ya ce masa, “Ai, ka gan shi, shi ne ma mai magana da kai.” 38 Sai ya ce, “Ya Ubangiji, na ba da gaskiya,” ya kuma yi masa sujada. 39 Yesu ya ce, “Na shigo duniyar nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.” 40 Da Farisiyawan nan da suke tare da shi suka ji haka, suka ce masa, “Wato, mu ma makafi ne?” 41 Yesu ya ce musu, “Ai, da makafi ne ku, da ba ku da zunubi. Amma da yake kun ce kuna gani, to, zunubinku ya tabbata.

Yahaya 10

Misali na Garken Tumaki

1 “Lalle hakika, ina gaya muku, wanda bai shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani wuri, to, shi ɓarawo ne, ɗan fashi kuma. 2 Wanda kuwa ya shiga ta ƙofar, makiyayin tumakin ne. 3 Mai tsaron ƙofar yakan buɗe masa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa, yakan kama sunan nasa tumakin, ya kai su waje. 4 Bayan ya fitar da dukan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin suna biye da shi, domin sun san muryarsa. 5 Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.” 6 Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su gane abin da ya faɗa musu ba.

Yesu ne Makiyayi Mai Kyau

7 Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. 8 Duk waɗanda suka riga ni zuwa cewa, su ne ni, ɓarayi ne, 'yan fashi kuma, amma tumakin ba su kula da su ba. 9 Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo. 10 Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace. 11 Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin. 12 Wanda yake ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso, sai ya watsar da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure waɗansu, ya fasa sauran. 13 Ya gudu ne fa, don shi ɗan asako ne, ba abin da ya dame shi da tumakin. 14 Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni, 15 kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin. 16 Ina kuma da waɗansu tumaki da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle ne in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda. 17 Domin wannan uba yake ƙaunata, domin ina ba da raina in ɗauko shi kuma. 18 Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarni ne daga wurin Ubana.” 19 Saboda maganar nan fa, sai rabuwa ta sāke shiga tsakanin Yahudawa. 20 Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?” 21 Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, wannan magana, ai, ba ta mai iska ba ce. Ashe, iska tana iya buɗe wa makaho ido?”

Yahudawa sun Ƙi Yesu

22 Lokacin idin tsarkakewa ne kuwa a Urushalima, 23 damuna ce kuma, Yesu kuwa yana zagawa a Shirayin Sulemanu cikin Haikali, 24 sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In dai kai ne Almasihun, ka gaya mana a fili.” 25 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata. 26 Amma ku ba ku gaskata ba, domin ba kwa cikin tumakina. 27 Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na. 28 Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su hallaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29 Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban. 30 Ni da Uba ɗaya muke.” 31 Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu su jajjefe shi. 32 Yesu ya amsa musu ya ce, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jajjefe ni?” 33 Yahudawa suka amsa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don sāɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah.” 34 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a Shari'arku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne?’ 35 To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su alloli (Nassi kuwa ba ya tashi), 36 kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, ‘Sāɓo kake,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’ 37 In ba ayyukan da Ubana yake yi nake yi ba, to, kada ku gaskata ni. 38 Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.” 39 Sai suka sāke ƙoƙarin kama shi, amma ya fita daga hannunsu. 40 Sa'an nan ya sāke komawa hayin Kogin Urdun, wurin da Yahaya ya fara yin baftisma, ya zauna a can, 41 mutane kuwa da yawa suka zo wurinsa, sai suka riƙa cewa, “Hakika, Yahaya bai yi wata mu'ujiza ba, amma duk abin da ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” 42 Nan fa mutane da yawa suka gaskata da shi.

Yahaya 11

Mutuwar Li'azaru

1 Wani mutum ne ya yi rashin lafiya, sunansa Li'azaru na Betanya, ƙauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Marta. 2 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan'uwanta Li'azaru ba shi da lafiya, ita ce wadda ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi, ta kuma shafe ƙafafunsa da gashinta. 3 To, 'yan'uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunar nan ba shi da lafiya.” 4 Da Yesu ya ji haka ya ce, “Wannan rashin lafiya, ƙarshensa ba mutuwa ba ne, domin a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurinsa.” 5 Yesu kuwa na ƙaunar Marta da 'yar'uwarta, da kuma Li'azaru. 6 To, da ya ji Li'azaru ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu. 7 Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.” 8 Almajiran suka ce masa, “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa suke neman jifanka, za ka sāke komawa can?” 9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa'a goma sha biyu ce yini ɗaya ba? Kowa yake tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyar nan. 10 Amma kowa yake tafiya da dare yakan yi tuntuɓe, don ba haske a gare shi!” 11 Ya faɗi haka, sa'an nan ya ƙara ce musu, “Amininmu Li'azaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi.” 12 Sai almajiran suka ce masa, “Ya Ubangiji, in dai barci ne ya ɗauke shi, ai, zai warke.” 13 Alhali kuwa, Yesu zancen mutuwar Li'azaru yake, amma su sun ɗauka yana nufin barcin hutawa ne. 14 Sai Yesu ya gaya musu a fili, ya ce, “Li'azaru dai ya mutu. 15 Ina kuwa farin ciki da ba na nan, saboda ku domin ku ba da gaskiya. Amma mu dai je wurinsa.” 16 Sai Toma, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ya ce wa 'yan'uwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”

Yesu shi ne Tashin Matattu da Rai Kuma

17 Da Yesu ya isa, ya tarar Li'azaru, har ya kwana huɗu a kabari. 18 Betanya kuwa kusa da Urushalima take, misalin mil biyu. 19 Yahudawa da yawa sun zo su yi wa Marta da Maryamu ta'aziyyar ɗan'uwansu. 20 Da jin Yesu yana zuwa, sai Marta ta je taryensa, Maryamu kuwa ta zauna a gida. 21 Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan'uwana bai mutu ba. 22 Ko yanzu ma na sani kome ka roƙi Allah zai yi maka.” 23 Yesu ya ce mata, “Ɗan'uwanki zai tashi.” 24 Marta ta ce masa, “Na sani zai tashi a tashin matattu a ranar ƙarshe.” 25 Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu. 26 Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?” 27 Ta ce masa, “I, ya Ubangiji. Na gaskata kai ne Almasihu, Ɗan Allah, wanda yake zuwa cikin duniya.”

Yesu ya yi Hawaye

28 Da ta faɗi haka, ta je ta kirawo 'yar'uwarta Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Malam ya zo, yana kiranki.” 29 Ita kuwa da jin haka, ta yi maza ta tashi ta nufi wurinsa. 30 Yesu dai bai iso ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana wurin da Marta ta tarye shi. 31 Da Yahudawan da suke tare da ita a cikin gida, suna yi mata ta'aziyya, suka ga Maryamu ta yi maza ta tashi ta fita, suka bi ta, suna zaton za ta kabarin ne, ta yi kuka a can. 32 Da Maryamu ta iso inda Yesu yake, ta gan shi, sai ta faɗi a gabansa ta ce masa, “Ya Ubangiji, da kana nan da dan'uwana bai mutu ba.” 33 Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita su ma, suna kuka, sai ya nisa a ransa, ya yi juyayi gaya. 34 Ya kuma ce, “Ina kuka sa shi?” Suka ce masa, “Ya Ubangiji, zo ka gani.” 35 Sai Yesu ya yi kuka. 36 Don haka Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!” 37 Amma waɗansunsu suka ce, “Ashe, wanda ya buɗe wa makahon nan ido, ba zai iya hana wannan mutum mutuwa ba?”

Yesu ya Ta da Li'azaru daga Matattu

38 Sai Yesu ya sāke nisawa a ransa, ya iso kabarin. Kabarin kuwa kogon dutse ne, da wani dutse kuma an rufe bakin. 39 Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Sai Marta, 'yar'uwar mamacin, ta ce masa, “Ya Ubangiji, ai, yanzu ya yi ɗoyi, don yau kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.” 40 Sai Yesu ya ce mata, “Ban gaya miki ba, in kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah?” 41 Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni. 42 Ko dā ma na sani koyaushe kana saurarona, amma na faɗi haka ne saboda jama'ar da suke nan tsaitsaye, domin su gaskata kai ne ka aiko ni.” 43 Da ya faɗi haka ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li'azaru fito!” 44 Sai mamacin ya fito, ƙafa da hannu a ɗaure da likkafani, fuskarsa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce musu, “Ku kwance masa, ya tafi.”

An Kulla Shawara gāba da Yesu

45 Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da ya yi, suka gaskata da shi. 46 Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47 Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara 'yan majalisa, suka ce, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu'ujizai da yawa haka? 48 In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama'armu.” 49 Amma ɗayansu, mai suna Kayafa, wanda yake shi ne babban firist a shekarar nan, ya ce musu, “Ku dai ba ku san kome ba. 50 Ba kwa lura, ai, ya fiye muku mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a, da duk al'umma ta hallaka.” 51 Ba da nufinsa ya faɗi haka ba, sai dai da yake shi ne babban firist a shekarar nan, ya yi annabci cewa, Yesu zai mutu saboda jama'a, 52 ba ma saboda al'umma kaɗai ba, har ma yă tattaro 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina su zama ɗaya. 53 Daga ran nan fa sai suka ƙulla su kashe shi. 54 Saboda haka, Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba, amma ya tashi daga wurin, ya tafi ƙasar da take a bakin jeji, ya shiga wani gari, mai suna Ifraimu. Nan ya zauna da almajiran. 55 Ana nan, Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya gabato, mutane da yawa daga ƙauyuka suka tafi Urushalima su tsarkake kansa kafin idin. 56 Suka yi ta neman Yesu, suna tsaitsaye a Haikali, suna ce wa juna, “Me kuka gani? Zai zo idin kuwa?” 57 Don dā ma, manyan firistoci da Farisiyawa sun yi umarni, cewa, idan kowa ya san inda Yesu yake, ya zo ya faɗa, su kama shi.

Yahaya 12

An Shafi Yesu da Man Ƙanshi a Betanya

1 Idin Ƙetarewa sauran kwana shida, sai Yesu ya zo Betanya inda Li'azaru yake, wanda Yesu ya tasa daga matattu. 2 Nan aka yi masa abincin dare, Marta ce ta yi hidima, Li'azaru kuwa yana cikin masu ci tare da shi. 3 Sai Maryamu ta ɗauko awo guda na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tamanin gaske, ta shafa a ƙafafun Yesu, sa'an nan ta shafe su da gashinta. Duk gidan ya game da ƙanshin man. 4 Amma Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wato, wanda zai bāshe shi, ya ce, 5 “Me ya hana a sayar da man nan a kan dinari ɗari uku, a ba talakawa kuɗin?” 6 Ya faɗi haka fa, ba don yana kula da talakawa ba, a'a, sai dai don shi ɓarawo ne, da yake kuma jakar kuɗinsu tana hannunsa, yakan riƙa taɓa abin da ke ciki. 7 Sai Yesu ya ce, “A ƙyale ta, dā ma ta ajiye shi domin tanadin ranar jana'izata. 8 Ai, kullum kuna tare da talakawa, amma ba kullum kuke tare da ni ba.”

An Ƙulla Shawara gāba da Li'azaru

9 Da taron Yahudawa mai yawa suka ji labari yana nan, sai suka zo, ba domin Yesu kaɗai ba, har ma don su ga Li'azaru wanda ya tasa daga matattu. 10 Sai manyan firistoci suka yi shawarar kashe Li'azaru, shi ma, 11 domin ta dalilinsa Yahudawa da yawa suke warewa, suna gaskatawa da Yesu.

Mutanen Urushalima sun Marabci Yesu

12 Kashegari babban taron da suka zo idi, da suka ji Yesu yana zuwa Urushalima, 13 suka ɗaɗɗauko gazarin dabino suka firfita taryensa, suna ta da murya suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila!” 14 Da Yesu ya sami wani aholaki sai ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa, 15 “Kada ki ji tsoro, yake 'yar Sihiyona, Ga sarkinki yana zuwa a kan aholakin jaki!” 16 Da fari almajiransa ba su gane abin nan ba, amma bayan an ɗaukaka Yesu, suka tuna abin nan a rubuce yake game da shi, har ma aka yi masa shi. 17 Taron da suke tare da shi sa'ad da ya kira Li'azaru yă fito daga kabari, ya tashe shi daga matattu, su suka riƙa shaidarwa da haka. 18 Shi ya sa taron suka fita taryensa, don sun ji ya yi mu'ujizan nan. 19 Sai Farisiyawa suka ce wa juna, “Duba! Ba abin da muka iya! Ai, duk duniya tana bayansa.”

Waɗansu Helenawa sun Nemi Yesu

20 To, a cikin waɗanda suka zo idin yin sujada akwai waɗansu Helenawa. 21 Sai suka zo wurin Filibus, mutumin Betsaida ta ƙasar Galili, suka roƙe shi suka ce, “Maigida, muna bukatar mu gana da Yesu.” 22 Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawas, Andarawas kuma ya zo da Filibus, suka gaya wa Yesu. 23 Yesu ya amsa musu ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum. 24 Lalle hakika, ina gaya muku, in ba an binne ƙwayar alkama ta mutu ba, za ta zauna ita kaɗai. Amma in ta mutu sai ta hayayyafa. 25 Mai ƙaunar ransa zai rasa shi. Wanda kuwa ya ƙi ransa a duniyar nan, ya kiyaye shi ke nan, har ya zuwa rai madawwami. 26 Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa yake bauta mini, Uba zai girmama shi.”

Lalle a Ɗaga Ɗan Mutum Sama

27 “Yanzu ina jin nauyi a raina. Me zan ce kuwa? In ce, ‘Ya Uba ka ɗauke mini wannan lokaci?’ A'a, ai, dā ma na zo ne takanas domin wannan lokaci. 28 Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi,” 29 Da taron da suke tsaya a wurin suka ji muryar, suka ce, “An yi cida.” Waɗansu kuwa suka ce, “Wani mala'ika ne ya yi masa magana.” 30 Yesu ya amsa ya ce, “Ba saboda ni aka yi wannan murya ba, sai dominku. 31 Yanzu ne za a yi wa duniyar nan shari'a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyar nan. 32 Ni kuwa bayan an ɗaga ni daga ƙasa zan ja dukan mutane gare ni.” 33 Ta faɗar haka ya kwatanta irin mutuwar da zai yi. 34 Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari'armu ta gaya mana, cewa, Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?” 35 Yesu ya ce musu, “Haske yana tare da ku har ɗan lokaci kaɗan na gaba. Ku yi tafiya tun haske yana tare da ku, kada duhu ya ci muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda yake tafiya ba. 36 Ku gaskata da hasken, tun kuna tare da shi, domin ku zama mutanen haske.” Yahudawa ba su Gaskata da shi Ba Yesu ya faɗi haka, sa'an nan ya tafi ya ɓuya musu. 37 Amma ko da yake ya sha yin mu'ujizai da yawa a gabansu, duk da haka, ba su gaskata shi ba, 38 domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu? Ga wa kuma aka bayyana ikon Ubangiji?” 39 Shi ya sa ba su iya ba da gaskiya ba. Domin Ishaya ya sāke cewa, 40 “Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciyarsu, Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci, Har su juyo gare ni in warkar da su.” 41 Ishaya ya faɗi haka saboda ya ga ɗaukakar Almasihu, ya kuma ba da labarinsa. 42 Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama'a. 43 Don sun fi ƙaunar girmamawar mutane da girmamawar Allah.

Maganar Yesu za ta yi Hukunci

44 Sai Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Wanda yake gaskatawa da ni, ba ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni. 45 Wanda kuma yake dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne. 46 Na zo duniya a kan ni haske ne, domin duk mai gaskatawa da ni kada ya yi zaman duhu. 47 Kowa ya ji maganata, bai kuwa kiyaye ta ba, ba ni nake hukunta shi ba. Gama ba don yi wa duniya hukunci na zo ba, sai dai domin in ceci duniya. 48 Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai hukunta shi, maganar da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe. 49 Ba kuwa domin kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa, da kuma maganar da zan yi. 50 Na kuma san umarnin nan nasa rai ne madawwami. Domin haka, abin da nake faɗa ina faɗa ne daidai yadda Uba ya faɗa mini.”

Yahaya 13

Yesu ya Wanke Ƙafafun Almajiransa

1 Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai bar wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa. 2 Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi. 3 Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma, 4 sai ya tashi daga cin abincin, ya ajiye mayafinsa, ya ɗauko mayani ya yi ɗamara da shi. 5 Sa'an nan ya zuba ruwa a daro, ya fara wanke ƙafafun almajiran, yana shafewa da mayanin. 6 Sai ya zo kan Bitrus, shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ashe, kai ne za ka wanke mini ƙafa?” 7 Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu kam, ba ka san abin da nake yi ba, amma daga baya za ka fahimta.” 8 Bitrus ya ce masa, “Wane ni! Ai, ba za ka wanke mini ƙafa ba har abada!” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo a gare ni.” 9 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kaɗai ba, har ma da hannuwana da kaina!” 10 Yesu ya ce masa, “Wanda ya yi wanka ba ya bukatar wanke kome, sai ƙafafunsa kawai, domin ya riga ya tsarkaka sarai. Ku ma tsarkakakku ne, amma ba dukanku ne ba.” 11 Don ya san wanda zai bāshe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukanku ne tsarkakakku ba.” 12 Bayan ya wanke ƙafafunsu, ya yafa mayafinsa, sai ya sāke kishingiɗa, ya ce musu, “Kun gane abin da na yi muku? 13 Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake. 14 Tun da yake ni da nake Ubangijinku, kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, kuma wajibi ne ku wanke wa juna. 15 Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku 16 Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi. 17 In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne. 18 Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda muke ci tare ya tasar mini.’ 19 Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi. 20 Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”

Yesu ya Ce za a Bāshe Shi

21 Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.” 22 Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa ko da wa yake. 23 Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu. 24 Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?” 25 Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne shi?” 26 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma 'yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma 'yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti. 27 Da karɓar 'yar lomar nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.” 28 Amma cikin waɗanda suke cin abinci, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. 29 Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba talakawa wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu. 30 Shi kuwa da karɓar 'yar lomar, sai ya fita, da dare ne kuwa.

Sabon Umarni

31 Bayan da ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa. 32 Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga zatinsa, nan da nan kuwa zai ɗaukaka shi. 33 Ya ku 'ya'yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu. 34 Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna. 35 Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” 13 .36 Bitrus zai Yi M�sun Sanin Yesu Bitrus zai Yi M�sun Sanin Yesu 36 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.” 37 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.” 38 Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi m�sun sanina sau uku.”

Yahaya 14

Yesu ne Hanya zuwa wurin Uban

1 “Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 A gidan Ubana akwai wurin zama da yawa. Da ba haka ba ne, da na faɗa muku, domin zan tafi in shirya muku wuri. 3 In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, ku ma ku zama kuna can. 4 Inda za ni kuwa kun san hanya.” 5 Sai Toma ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, ta yaya za mu san hanyar?” 6 Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina. 7 Da kun san ni, da kun san Ubana ma. Amma daga yanzu kun san shi, kun kuma gan shi.” 8 Sai Filibus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka nuna mana Uban, bukatarmu ta biya ke nan.” 9 Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba, Filibus! Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Nuna mana Uban?’ ” 10 Wato, ba ka gaskata cikin Uba nake ba, Uba kuma cikina? Maganar da nake faɗa muku, ba domin kaina nake faɗa ba, Uba ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa. 11 Ku gaskata ni, a cikin Uba nake, Uba kuma a cikina, ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan su kansu. 12 “Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskatawa da ni ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har ma, zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba. 13 Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan. 14 Kome kuke roƙo da sunana, zan yi shi.”

Alkawarin Zuwan Ruhu Mai Tsarki

15 “In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina. 16 Ni ma zan roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimako ya kasance tare da ku har abada. 17 Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam, kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku. 18 “Ba zan bar ku marayu ba, zan zo wurinku. 19 Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ni a raye nake, ku ma za ku rayu. 20 A ran nan ne fa za ku sani, ni a cikin Uba nake, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku. 21 Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.” 22 Sai Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce masa, “Ya Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu, ba ga duniya ba?” 23 Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24 Wanda ba ya ƙaunata, ba zai kiyaye maganata ba. Maganar da kuke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni. 25 “Duk wannan na faɗa muku ne tun muna tare. 26 Amma Mai Taimako, wato, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, shi ne zai koya muku kome, ya kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27 Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada ku ji tsoro. 28 Kun dai ji na ce muku zan tafi, in kuma dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. 29 To, yanzu na faɗa muku tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru, ku ba da gaskiya. 30 Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, domin mai mulkin duniyar nan yana zuwa, ba shi kuwa da wani hannu a kaina, 31 sai dai domin duniya tă sani ina ƙaunar Uban, ina kuma yin yadda Uba ya umarce ni, ku tashi mu tafi daga nan.”

Yahaya 15

Yesu ne Itacen Inabi na Hakika

1 “Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi. 2 Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa. 3 Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku. 4 Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya 'ya'ya shi kaɗai, sai ko yana haɗe da itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina. 5 Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin 'ya'ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba. 6 Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone. 7 In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku. 8 Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna 'ya'ya da yawa, ta haka, kuma zaku tabbata almajiraina. 9 Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, ku zauna cikin ƙaunar da nake muku. 10 In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini. 11 Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke. 12 “Wannan fa shi ne umarnina, cewa, ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13 Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato, mutum yă ba da ransa saboda aminansa. 14 Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku. 15 Nan gaba, ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana. 16 Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku. 17 Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.

Ƙiyayyar Duniya

18 “In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku. 19 Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20 Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, ‘Bawa ba ya fin ubangijinsa.’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma. 21 Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba. 22 Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu. 23 Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma. 24 Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu, da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka. 25 An yi wannan kuwa domin a cika maganar da take a rubuce a cikin Shari'arsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’ 26 Amma sa'ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato, Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni. 27 Ku ma shaida ne, domin tun farko kuke tare da ni.

Yahaya 16

1 “Na faɗa muku waɗannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe. 2 Za su fisshe ku daga jama'a. Hakika, lokaci ma yana zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi. 3 Za su yi haka ne kuwa, domin ba su san Uba ko ni ba. 4 Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.”

Aikin Ruhu Mai Tsarki

“Ban faɗa muku abubuwan tun da farko ba, domin ina tare da ku. 5 Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ 6 Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku. 7 Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. 8 Sa'ad da kuwa ya zo zai kā da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci. 9 Wato, a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba, 10 a kan adalci kuwa, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba, 11 a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci. 12 “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba. 13 Sa'ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku a cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al'amuran da za su auku. 14 Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku. 15 Duk abin da Uba yake da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.”

Baƙin Ciki zai Koma Farin Ciki

16 “Bayan ɗan lokaci kaɗan, ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, za ku gan ni.” 17 Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni?’ da kuma cewa, ‘Domin za ni wurin Uba?’ ” 18 Suka ce, “Me yake nufi da, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan’ ɗin? Ai, ba mu san abin da yake faɗi ba.” 19 Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato, kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni?’ 20 Lalle hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21 Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya. 22 Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa'an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku. 23 A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana. 24 Har yanzu dai, ba ku roƙi komi cikin sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”

Na yi Nasara da Duniya

25 “Duk waɗannan na faɗa muku da misalai ne. Lokaci yana zuwa da ba zan ƙara faɗa muku kome da misalai ba, sai dai in ba ku labarin Uba a sarari. 26 A ran nan za ku yi roƙo a cikin sunana. Ban kuwa ce muku zan roƙar muku Uba ba, 27 domin shi Uban kansa na ƙaunarku, domin kun ƙaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito. 28 Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.” 29 Sai almajiransa suka ce, “Yauwa! Yanzu ne fa kake magana a sarari, ba da misali ba. 30 Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.” 31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, yanzu kun gaskata? 32 To, lokaci yana zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba yana tare da ni. 33 Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”

Yahaya 17

Addu'ar Yesu don Almajiransa

1 Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka, 2 tun da ka ba shi iko a kan dukkan 'yan adam, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3 Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko. 4 Na ɗaukaka ka a duniya da yake na cika aikin da ka ba ni in yi. 5 Yanzu kuma, ya Uba, ka ɗaukaka ni zuwa ga zatinka da ɗaukakar nan da nake da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasance. 6 “Na bayyana sunanka ga mutanen da ka ba ni daga cikin duniya. Dā ma naka ne, ka kuwa ba ni su, sun kuma kiyaye maganarka. 7 Yanzu kuwa sun san duk iyakar abin da ka ba ni daga gare ka yake. 8 Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni. 9 Ni, roƙo nake yi dominsu. Ba duniya nake roƙar wa ba, sai dai su waɗanda ka ba ni, domin su naka ne. 10 Dukkan nawa naka ne, duk naka kuma nawa ne, an kuma ɗaukaka ni a zukatansu. 11 Yanzu kuma ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai tsarki, ka kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni, su zama ɗaya kamar yadda muke. 12 Duk sa'ad da nake tare da su, na kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni. Na kāre su, ba kuwa waninsu da ya hallaka, sai dai hallakakken nan, domin Nassi ya cika. 13 Amma a yanzu ina zuwa wurinka. Ina faɗar wannan magana tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu. 14 Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15 Ba na roƙonka ka ɗauke su daga duniya, sai dai ka kāre su daga Mugun nan. 16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17 Ka tsarkake su cikin gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya. 18 Kamar yadda ka aiko ni duniya, haka ni ma na aike su duniya. 19 Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya. 20 “Ba kuwa waɗannan kaɗai nake roƙar wa ba, har ma masu gaskatawa da ni ta wurin maganarsu, 21 domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu, domin duniya ta gaskata, cewa, kai ne ka aiko ni. 22 Ɗaukakar da ka yi mini, ita na yi musu, domin su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya, 23 ni a cikinsu, kai kuma a cikina, domin su zama ɗaya sosai, duniya ta gane kai ne ka aiko ni, ta kuma gane ka ƙaunace su kamar yadda ka kaunace ni. 24 Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba. 25 Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta san ka ba, amma ni na san ka, waɗannan kuma sun sani kai ne ka aiko ni. 26 Na sanar da su sunanka, zan kuma ci gaba da sanar masu, domin ƙaunar da ka yi mini tă kasance a cikinsu, ni ma in kasance a cikinsu.”

Yahaya 18

An Ba da Yesu, an Kama Shi

1 Bayan da Yesu ya yi maganar nan, ya fita, shi da almajiransa zuwa hayin Rafin Kidron, inda wani lambu yake, ya kuma shiga da almajiransa. 2 Yahuza ma wanda ya bāshe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba haɗuwa da almajiransa a can. 3 Yahuza kuwa bayan ya ɗauko ƙungiyar soja, da waɗansu dogaran Haikali daga manyan firistoci da Farisiyawa, suka zo wurin, riƙe da fitilu, da jinyoyi, da makamai, 4 Yesu kuwa da ya san duk abin da zai same shi, ya yiwo gaba, ya ce musu, “Wa kuke nema?” 5 Suka amsa masa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce musu, “Ni ne.” Yahuza kuwa da ya bāshe shi yana tsaye tare da su. 6 Da Yesu ya ce musu, “Ni ne,” suka ja da baya da baya, har suka fāɗi. 7 Sai ya sāke tambayarsu, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.” 8 Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku, ni ne. In kuwa ni kuke nema, ku bar waɗannan su tafi.” 9 Wannan kuwa domin a cika maganar da ya yi ne cewa, “A cikin waɗanda ka ba ni ban yar da ko ɗaya ba.” 10 Bitrus kuwa da yake yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunnensa na dama. Sunan bawan Malkus. 11 Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Mai da takobinka kube. Ba sai in sha ƙoƙon da Uba ya ba ni in sha ba?”

Yesu a gaban Babban Firist

12 Sai ƙungiyar soja da shugabansu, da dogaran nan na Yahudawa suka kama Yesu, suka ɗaure shi, 13 suka tafi da shi wurin Hanana da fari, don shi surukin Kayafa ne, wanda yake shi ne babban firist a shekarar nan. 14 Kayafa kuwa shi ne ya yi wa Yahudawa shawara, cewa, ya fiye musu mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a. 18 .15 Bitrus ya Yi M�sun Sanin Yesu Bitrus ya Yi M�sun Sanin Yesu 15 Sai Bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajiri. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har gidan firist ɗin tare da Yesu, 16 Bitrus kuwa ya tsaya a bakin ƙofa daga waje. Sai ɗaya almajirin da yake sananne ga babban firist ya fita, ya yi magana da wanda yake jiran ƙofa, sa'an nan ya shigo da Bitrus. 17 Baranyar da yake jiran ƙofar kuwa ta ce wa Bitrus, “Anya! Kai ma ba a cikin almajiran mutumin nan kake ba?” Ya ce, “A'a, ba na ciki.” 18 To, barori da dogaran Haikali kuwa sun hura wutar gawayi, don ana sanyi, suna tsaitsaye, suna jin wutar. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin wutar.

Babban Firist ya Tuhumi Yesu

19 Sai babban firist ya tuhumi Yesu a kan almajiransa da kuma koyarwarsa. 20 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba. 21 Don me kake tuhumata? Tuhumi waɗanda suka saurare ni a kan abin da na faɗa musu, ai, sun san abin da na faɗa.” 22 Da ya faɗi haka, wani daga cikin dogaran da suke tsaye kusa, ya mari Yesu, ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?” 23 Yesu ya amsa masa ya ce, “In na faɗi mugun abu to, ka ba da shaida kan haka. In kuwa daidai na faɗa, to, don me za ka mare ni?” 24 Sai Hanana ya aika da shi a ɗaure wurin Kayafa, babban firist. 18 .25 Bitrus ya Sāke M�sun Sanin Yesu Bitrus ya Sāke M�sun Sanin Yesu 25 To, Bitrus kuwa yana tsaye yana jin wuta. Sai suka ce masa, “Anya! Kai ma ba a cikin almajiransa kake ba?” Sai ya yi m�su ya ce, “A'a, ba na ciki.” 26 Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato, dangin wanda Bitrus ya fille wa kunne, ya ce, “Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba?” 27 Sai Bitrus ya sāke yin m�su. Nan da nan kuwa zakara ya yi cara.

Yesu a gaban Bilatus

28 Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fādar mai mulki. Da asuba ne kuwa. Su kansu ba su shiga fādar ba, don kada su ƙazantu su kāsa cin jibin Ƙetarewa. 29 Saboda haka, Bilatus ya fito wajensu, ya ce, “Wace ƙara kuka kawo ta mutumin nan?” 30 Sai suka amsa masa suka ce, “Da wannan ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bāshe shi gare ka ba.” 31 Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!” Sai Yahudawa suka ce masa, “Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa a kan kowa.” 32 Wannan kuwa don a cika maganar da Yesu ya yi ne, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi. 33 Sai Bilatus ya koma cikin fāda, ya kira Yesu ya ce masa, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” 34 Yesu ya amsa ya ce, “Wato, wannan faɗarka ce, ko kuwa waɗansu ne suka ce da ni haka a wurinka?” 35 Bilatus ya amsa ya ce, “Ni Bayahude ne? Ai, jama'arku da manyan firistoci su ne suka bāshe ka gare ni. Me ka yi?” 36 Yesu ya amsa ya ce, “Mulkina ba na duniyar nan ba ne. Da mulkina na duniyar nan ne da barorina za su yi yaƙi kada a bāshe ni ga Yahudawa. Amma hakika, mulkina ba daga nan yake ba.” 37 Sai Bilatus ya ce masa, “Wato, ashe, sarki ne kai?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa, ni sarki ne. Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya. Kowane mai ƙaunar gaskiya kuwa yakan saurari muryata.” 38 Bilatus ya ce masa, “Wane abu ne, shi gaskiya?”

An Hukunta wa Yesu Mutuwa

Bayan da ya faɗi haka, ya sāke fitowa wurin Yahudawa, ya ce musu, “Ni kam, ban same shi da wani laifi ba. 39 Amma dai kuna da wata al'ada, in Idin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku mutum ɗaya. To, kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?” 40 Sai suka sāke ɗaukar kururuwa suna cewa, “A'a, ba wannan ba, sai dai Barabbas!” Barabbas ɗin nan kuwa ɗan fashi ne.

Yahaya 19

1 Sa'an nan Bilatus ya sa a tafi da Yesu, a yi masa bulala. 2 Sai soja suka yi wani kambi na ƙaya suka sa masa a kā, suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan shunayya. 3 Suka yi ta zuwa wurinsa, suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” suna ta marinsa. 4 Sai Bilatus ya sāke fitowa, ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi, domin ku san ban same shi da wani laifi ba.” 5 Sa'an nan Yesu ya fito, sāye da kambin ƙayar, da alkyabba mai ruwan shunayya. Sai Bilatus ya ce musu, “To, ga mutumin!” 6 Da manyan firistoci da dogaran Haikali suka gan shi, suka ɗau kururuwa suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi ku da kanku, ku gicciye shi, ni kam, ban same shi da wani laifi ba.” 7 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Shari'a, bisa ga Shari'ar nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.” 8 Da Bilatus ya ji maganar nan sai ya ƙara tsorata. 9 Ya sāke shiga fāda, ya ce wa Yesu, “Daga ina kake?” Amma Yesu bai amsa masa ba. 10 Saboda haka Bilatus ya ce masa, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka sani ba ni ne da ikon sakinka, ko gicciye ka?” 11 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina in ba an ba ka daga Sama ba, saboda haka wanda ya bāshe ni gare ka ya fi ka zunubi.” 12 A kan wannan Bilatus ya nema ya sake shi, sai dai Yahudawa suka ɗau kururuwa suna cewa, “In dai ka saki wannan, kai ba masoyin Kaisar ba ne. Ai, kowa ya mai da kansa sarki, ya tayar wa Kaisar ke nan.” 13 Da Bilatus ya ji wannan magana, sai ya fito da Yesu, ya zauna a kan gadon shari'a, wurin da ake kira Daɓe, da Yahudanci kuwa, Gabbata. 14 Ran nan kuwa ranar shirin Idin Ƙetarewa ce, wajen tsakiyar rana. Sai ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku!” 15 Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu ba mu da sarki sai Kaisar.” 16 Sa'an nan ya bāshe shi gare su su gicciye shi.

An Gicciye Yesu

17 Sai suka tafi da Yesu. Ya kuwa fita, shi kansa yake ɗauke da gicciyensa, har zuwa wurin da ake kira Wurin Ƙoƙon Kai, da Yahudanci kuwa, Golgota. 18 Nan suka gicciye shi, da kuma waɗansu mutum biyu tare da shi, ɗaya ta kowane gefe, Yesu kuwa a tsakiya. 19 Bilatus kuma ya rubuta wata sanarwa, ya kafa ta a kan gicciyen. Abin da aka rubuta ke nan, “Yesu Banazare Sarkin Yahudawa.” 20 Yahudawa da yawa kuwa sun karanta wannan sanarwa, domin wurin da aka gicciye Yesu kusa da birni ne. An kuwa rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da kuma Helenanci. 21 Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce wa Bilatus, “Kada ka rubuta ‘Sarkin Yahudawa,’ sai dai ka rubuta, ‘A faɗarsa shi ne Sarkin Yahudawa.’ ” 22 Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta na rubuta ke nan.” 23 Bayan soja sun gicciye Yesu, suka ɗibi tufafinsa, suka kasa kashi huɗu, kowane soja ya ɗauki kashi guda. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta. 24 Sai suka ce wa juna, “Kada mu tsaga ta, sai dai mu yi kuri'a a kanta, mu ga wanda zai ci.” Wannan kuwa domin a cika Nassi ne cewa, “Suka rarraba tufafina a tsakaninsu, suka jefa kuri'a akan rigata” 25 Haka fa sojan suka yi. To, kusa da gicciyen Yesu kuwa da mahaifiyarsa, da 'yar'uwarta, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya, suna tsaye. 26 Da Yesu ya ga mahaifiyarsa, da almajirin nan da yake ƙauna suna tsaye kusa, ya ce wa mahaifiyarsa, “Iya, ga ɗanki nan!” 27 Sa'an nan ya ce wa almajirin, “Ga tsohuwarka nan!” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.

Mutuwar Yesu

28 Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama kome, domin a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.” 29 To, akwai wani gora cike da ruwan tsami a ajiye a nan. Sai suka jiƙa soso da ruwan tsamin, suka soka a sandan izob suka kai bakinsa. 30 Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin nan ya ce, “An gama!” Sa'an nan ya sunkuyar da kansa ya ba da ransa.

An Soki Kwiɓin Yesu

31 Da yake ran nan ranar shiri ce, don kada a bar jikuna a gicciye ran Asabar (domin wannan Asabar ɗin babbar rana ce), sai Yahudawa suka roƙi Bilatus a karya ƙafafunsu, a kuma ɗauke jikunan. 32 Sai soja suka zo suka karya ƙafafun na farkon nan, da kuma na ɗayan da aka gicciye tare da shi. 33 Amma da suka zo wurin Yesu, suka kuma ga ya riga ya rasu, ba su karya ƙafafunsa ba. 34 Sai dai ɗaya daga cikin sojan nan ya soke shi da mashi a kwiɓi, nan da nan sai ga jini da ruwa suka gudano. 35 Wanda ya gani ɗin kuwa shi ya ba da shaida kan haka, shaidarsa kuwa gaskiya ce, ya kuma san gaskiya yake faɗa, domin ku ma ku ba da gaskiya. 36 Wannan kuwa don a cika Nassi ne cewa, “Ko ƙashinsa ɗaya ba za a karya ba.” 37 Wani Nassi kuma ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”

Jana'izar Yesu

38 Bayan haka Yusufu, mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne amma a ɓoye domin tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus izinin ɗauke Yesu. Bilatus kuwa ya ba shi izini, ya kuwa zo ya ɗauke jikin Yesu. 39 Nikodimu kuma, wanda zuwansa na farko wurin Yesu da dad dare ne, ya zo da mur da al'ul a gauraye, wajen awo ɗari. 40 Sai suka ɗauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lilin game da kayan ƙanshin nan, bisa ga al'adar Yahudawa ta jana'iza. 41 A wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma da wani sabon kabari wanda ba a taɓa sa kowa a ciki ba. 42 Da yake ranar shiri ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka sa Yesu a nan.

Yahaya 20

Tashin Yesu daga Matattu

1 To, a ranar farko ta mako, Maryamu Magadaliya ta je kabarin da asuba, tun da sauran duhu, ta ga an kawar da dutsen daga kabarin. 2 Sai ta yiwo gudu wurin Bitrus da kuma almajirin nan da Yesu yake ƙauna, ta ce musu, “An ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuwa san inda aka sa shi ba.” 3 Sai Bitrus da almajirin nan suka fita suka doshi kabarin. 4 Duka biyu suka ruga a guje, amma almajirin nan ya tsere wa Bitrus, ya riga isa kabarin. 5 Yana duƙawa yana leƙa ciki, sai ya ga likkafanin lilin a ajiye, amma fa bai shiga ba. 6 Sa'an nan Bitrus ya zo a bayansa, ya kuwa shiga kabarin, ya ga likkafanin a ajiye, 7 mayanin kuma da yake kansa ba a ajiye tare da likkafanin yake ba, amma a naɗe shi kaɗai a waje ɗaya. 8 Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga, ya gani, ya kuma ba da gaskiya. 9 Don kafin lokacin nan ba su fahimci Nassin nan ba, cewa, lalle ne yă tashi daga matattu. 10 Sai almajiran suka koma gida.

Yesu ya Bayyana ga Maryamu Magadaliya

11 Maryamu kuwa tana tsaye a bakin kabarin daga waje, tana kuka. Tana cikin kuka sai ta duƙa, ta leƙa kabarin, 12 sai ta ga mala'iku biyu saye da fararen tufafi a zaune inda dā gawar Yesu take, ɗaga wajen kai, ɗaya kuwa wajen ƙafafu. 13 Suka ce mata, “Uwargida, don me kike kuka?” Ta ce musu, “Ai, an ɗauke Ubangijina, ban kuwa san inda aka sa shi ba.” 14 Da ta faɗi haka sai ta juya ta ga Yesu tsaye, amma ba ta gane Yesu ne ba. 15 Yesu ya ce mata, “Uwargida, don me kike kuka? Wa kuma kike nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.” 16 Yesu ya ce mata, “Maryamu!” Sai ta juya ta ce masa da Yahudanci, “Rabboni!” wato, Malam. 17 Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin 'yan'uwana ki ce musu ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.” 18 Sai Maryamu Magadaliya ta je ta ce wa almajiran, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma ce shi ya faɗa mata waɗannan abubuwa.

Yesu ya Bayyana ga Almajiransa

19 A ran nan da magariba, ranar farko ta mako, ƙofofin ɗakin da almajiran suke ciki yana kulle sabo da tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce musu, “Salama a gare ku!” 20 Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da kwiɓinsa. Sai almajiran suka yi farin ciki da ganin Ubangiji. 21 Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama a gare ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma na aike ku.” 22 Da ya faɗi haka ya busa musu numfashinsa, ya ce musu, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23 Duk waɗanda kuka gafarta wa zunubansu, an gafarta musu ke nan. Duk waɗanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta ba ke nan.”

Rashin Bangaskiyar Toma

24 Toma kuwa, ɗaya daga cikin goma sha biyun nan, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ba ya nan tare da su sa'ad da Yesu ya zo. 25 Sai sauran almajiran suka ce masa, “Mun ga Ubangiji.” Amma ya ce musu, “In ban ga gurbin ƙusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsata a gurbin ƙusoshin, in kuma sa hannuna a kwiɓinsa ba, ba zan ba da gaskiya ba.” 26 Bayan kwana takwas har wa yau almajiransa na cikin gidan, Toma ma yana nan tare da su, ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce, “Salama a gare ku.” 27 Sa'an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan, ka ji hannuwana. Miƙo hannunka kuma ka sa a kwiɓina. Kada ka zama marar ba da gaskiya, sai dai mai ba da gaskiya.” 28 Toma ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangijina da kuma Allahna!” 29 Sai Yesu ya ce masa, “Wato, saboda ka gan ni ka ba da gaskiya? Albarka tā tabbata ga waɗanda ba su gani ba, amma kuwa suka ba da gaskiya.”

Manufar Littafin Nan

30 Yesu ya yi waɗansu mu'ujizai da yawa dabam dabam a gaban almajiran, waɗanda ba a rubuta a littafin nan ba. 31 Amma an rubuta waɗannan ne, domin ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai a cikin sunansa.

Yahaya 21

Yesu ya Bayyana ga Almajirai Bakwai

1 Bayan haka Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiran a bakin Tekun Tibariya. Ga kuwa yadda ya bayyana kansa. 2 Bitrus, da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai, da Nata'ala na Kana ta ƙasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma waɗansu almajiransa biyu, duk suna nan tare, 3 Sai Bitrus ya ce musu, “Za ni s�.” Suka ce masa, “Mu ma mā tafi tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi. Amma a daren nan ba su kama kome ba. 4 Gari yana wayewa sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran ba su gane Yesu ne ba. 5 Sai Yesu ya ce musu, “Samari, kuna da kifi?” Suka amsa masa suka ce, “A'a.” 6 Ya ce musu, “Ku jefa taru dama da jirgin za ku samu.” Suka jefa, har suka kāsa jawo shi don yawan kifin. 7 Sai almajirin nan da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ubangiji ne fa!” Da Bitrus ya ji, ashe, Ubangiji ne sai ya yi ɗamara da taguwarsa, don a tuɓe yake, ya fāɗa tekun. 8 Sauran almajirai kuwa suka zo a cikin ƙaramin jirgi, janye da tarun cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, kamar misalin kamu ɗari biyu ne. 9 Da fitowarsu gaci sai suka ga garwashi a wurin, da kifi, da kuma gurasa. 10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifi daga cikin waɗanda kuka kama yanzu.” 11 Sai Bitrus ya hau jirgin, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku. Amma duk da yawansu haka, tarun bai kece ba. 12 Sai Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Daga cikin almajiran kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin tambayarsa ko shi wane ne, domin sun sani Ubangiji ne. 13 Sai Yesu ya zo ya ɗauki gurasar, ya ba su, haka kuma kifin. 14 Wannan ne fa zuwa na uku da Yesu ya bayyana ga almajiran bayan an tashe shi daga matattu.

Yi Kiwon Tumakina

15 Da suka karya kumallo Yesu ya ce wa Bitrus, “Bitrus ɗan Yahaya, ka fi waɗannan ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon 'ya'yan tumakina.” 16 Ya sāke faɗa masa, faɗa ta biyu, “Bitrus ɗan Yahaya, kana ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka kiyaye tumakina.” 17 Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina. 18 Lalle hakika, ina gaya maka, lokacin samartakarka kakan yi wa kanka ɗamara, ka tafi inda ka nufa, amma in ka tsufa, za ka miƙe hannuwanka, wani ya yi maka ɗamara, ya kai ka inda ba ka nufa ba.” 19 (Ya faɗi wannan ne yana kwatanta irin mutuwar da Bitrus zai yi ya ɗaukaka Allah.) Bayan ya faɗi haka, ya ce masa, “Bi ni.”

Almajirin da Yesu yake Ƙauna

20 Sai Bitrus ya waiwaya ya ga almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana biye da su, wato, wanda ya jingina gab da Yesu lokacin cin jibin nan da ya ce, “Ya Ubangiji, wane ne zai bāshe ka?” 21 Da Bitrus ya gan shi, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, wannan fa?” 22 Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai, bi ni!” 23 Saboda haka maganar nan ta bazu cikin 'yan'uwa, cewa, almajirin nan ba zai mutu ba. Alhali kuwa Yesu bai ce masa ba zai mutu ba, ya dai ce, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki?” 24 Wannan shi ne almajirin da yake ba da shaida a kan waɗannan al'amura, ya kuma rubuta su, mun kuwa sani shaidarsa tabbatacciya ce. 25 Akwai waɗansu ayyuka kuma masu yawa da Yesu ya aikata, in da za a rubuta ko wannensu ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.





AMAZING GRACE BIBLE INSTITUTE